Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da jerin sunayen mutum 223 da za su kasance cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai duk da yawan sunayen da aka saka cikin kwamitin, an lura da cewa wasu fitattun ’yan siyasar jam’iyyar APC ba su cikin jerin.
Daga cikin fitattun ’yan siyasar da ba a ga sunayensu a kwamitin ba akwai:
- Simon Lalong – Tsohon gwamnan Filato kuma tsohon shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2023.
- Yahaya Bello – Tsohon gwamnan Kogi wanda ya taka rawa wajen tallata APC da kuma kamfen Tinubu a zaɓen 2023.
- Festus Keyamo – Ministan Sufuri kuma tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a lokacin zaɓen 2019.
- Gbenga Daniel – Tsohon gwamnan Ogun wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
- Ibikunle Amosun – Tsohon gwamnan Ogun kuma Sanatan Ogun ta Tsakiya.
- Osagie Ize-Iyamu – Fitaccen ɗan siyasar Edo kuma ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin APC a baya.
- Dikko Umaru Radda – Gwamnan Jihar Katsina, wanda duk da kasancewarsa gwamna mai ci ba a saka sunansa cikin babban kwamitin ba.
- Abba Kabir Yusuf – Gwamnan Kano, wanda shi ma ba a ga sunansa cikin jerin mutum 223 na babban kwamitin yaƙin neman zaɓen ba.
- Nuhu Ribadu – Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro kuma tsohon babban jami’in kamfen APC a zaɓen da ya gabata.
- Timipre Sylva – Tsohon ministan man fetur kuma tsohon gwamnan Bayelsa.
- Ahmad Lawan – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi tikitin APC a zaɓen fid da gwani na 2023.
- Benjamin Kalu – Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai kuma ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC a Kudu maso Gabas.
Cire ko rashin saka wasu daga cikin waɗannan manyan ’yan siyasa ya haifar da ce-ce-ku-ce a wasu ɓangarorin jam’iyyar, musamman ganin irin rawar da wasu daga cikinsu suka taka a kamfen ɗin 2023.
A gefe guda kuma, an samu suka kan kasancewar wasu mutane cikin kwamitin, yayin da wasu ke tambayar dalilin da ya sa aka ware wasu fitattun ’yan jam’iyyar daga babban kwamitin.
Tsohon Sanata Dino Melaye ya kuma bayyana aniyarsa ta kalubalantar wasu nade-naden da aka yi cikin kwamitin a gaban kotu.
Shugaban Ƙasa Tinubu ya nada tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027.