Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaZan dawo da tallafin man fetur idan kun zabe ni - Sowore

Zan dawo da tallafin man fetur idan kun zabe ni – Sowore

Sowore ya ce zai magance zurarewar kudin tallafin man fetur bayan an dawo da shi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

Sowore ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Arise News a ranar Talata, inda ya ce cire tallafin man fetur ya kara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki.

Ya ce gwamnati za ta iya ci gaba da biyan tallafin tare da dakile cin hanci da rashawa da almundahana da ake zargin suna tattare da tsarin.

Sowore ya ce matsalar ba tallafin ba ce, illa cin hanci da rashawa da kuma yadda wasu ke amfani da tsarin wajen wawure kudaden gwamnati.

Ya kuma ce ya bayyana tsare-tsarensa kan yadda gwamnatinsa za ta samar da kudaden da za a biya tallafin a cikin manufofinsa.

Dan takarar ya ce zai farfado da matatun man fetur guda hudu na Najeriya tare da kara tace danyen mai a cikin gida domin rage kudin shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje.

Ya ce idan aka fara tace man fetur a cikin gida, za a rage kudin da gwamnati ke kashewa wajen shigo da mai, musamman ganin yadda Najeriya ke amfani da kusan lita miliyan 60 na man fetur a kullum.

Sowore ya kuma yi alkawarin tabbatar da cewa duk kudin da gwamnati za ta ware domin tallafin man fetur ya isa ga ‘yan kasa, tare da kawar da abin da ya kira “cabal” da ke cin moriyar tsarin.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci shigo da man fetur na bogi ko kuma yin ikirarin an shigo da man da bai iso Najeriya ba ba.

Sowore ya ce a matsayinsa na dan jarida a baya, ya taba fallasa badakalar tallafin man fetur, ciki har da wani rahoto da ya nuna yadda aka rubuta cewa wani jirgin ruwa ya shigo da man fetur Najeriya duk da cewa jirgin ya nutse shekaru 10 kafin hakan.

Ya ce irin wannan almundahana ba za ta samu gurbi a gwamnatinsa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments