Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, yana mai bayyana al’ummar Hausawa a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa haɗin kan Najeriya da ci gabanta.
Shugaba Tinubu ya ce Hausawa na taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka haɗin kai da bunƙasar ƙasa, musamman ta fuskar harshe, al’adu da hulɗar zamantakewa.
Ya bayyana harshen Hausa a matsayin ɗaya daga cikin manyan harsunan da suka bunƙasa, wanda ya zama muhimmin hanyar sadarwa, haɗin kai da gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya da sauran sassan duniya.
Shugaban ya ƙara da cewa Ranar Hausa wata dama ce ta girmama harshen Hausa da kuma al’ummar da ke amfani da shi wajen sadarwa, yada al’adu da kuma haɗa kan jama’a.
Ranar Hausa dai ana bikin ta ne a ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara, domin jaddada muhimmancin harshen Hausa da al’adun Hausawa.