Gwamnatin Jihar Kano ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ƙara samar mata da allurar rigakafin cutar mashako wato ‘diphtheria’ domin gudanar da gangamin yin rigakafi a faɗin jihar.
Darakta-Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Abbas, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a daren Talata.
Taron ya biyo bayan rahoton ɓarkewar cutar mashako a Rano da wasu ƙananan hukumomin jihar, lamarin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce ya yi sanadin mutuwar sama da yara 50.
Farfesa Abbas ya ce tuni jihar ta rubuta wa Gwamnatin Tarayya domin neman ƙarin alluran rigakafin.
“Jihar Kano ta rubuta wa Gwamnatin Tarayya domin samun ƙarin allurai don mu yi wa mutanenmu rigakafi,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar, musamman iyaye, da su gaggauta kai duk wanda ke nuna alamun diphtheria ko wata cuta zuwa cibiyar lafiya domin samun magani cikin lokaci.
“Muna roƙon iyaye da su kai rahoto da wuri. Kai mutum cibiyar lafiya da wuri shi ne abin da ke ceton rai. Kuma ko ba cuta ba ce, duk wata matsala, musamman idan ta daɗe kuma ta rikice, magance ta na da wahala. Don haka, ku je cibiyar lafiya mafi kusa da ku. Idan lamarin ya shafi cututtukan da ka iya yaɗuwa, za su sanar da mu,” in ji shi.
Daraktan ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke kasa kai rahoton masu fama da cututtuka zuwa asibitoci, yana mai cewa akwai jami’an sa ido da sanar da cututtuka 126 da aka tura zuwa ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce abin takaici ne yadda ake samun mutane masu fama da cutar har sama da 50 ba tare da an kai rahotonsu asibiti ba.
“Don haka, abin takaici ne matuƙa mu samu mutane da suka kai 50 ba a kai rahotonsu asibiti ba. Muna roƙon mutane da su zo asibitoci da cibiyoyin lafiya. Idan asibitocin suka ga adadin masu fama da cutar ya fi ƙarfin abin da za su iya kula da shi, za su turo mana su, kuma za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji shi.
Farfesa Abbas ya ce cibiyar ta daɗe tana sa ido kan cutar mashako tun bayan zuwan gwamnatin Gwamna Abba Yusuf.
Ya bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa yanzu, an samu sama da mutane 38,000 da ake zargi da kamuwa da cutar, yayin da sama da 31,000 daga cikinsu aka tabbatar sun kamu.
Sai dai ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne, sama da kashi 55 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar yara ne da ba su taɓa samun ko wane irin rigakafi ba.
Ya ƙara da cewa sama da kashi 16 cikin 100 sun samu wani ɓangare na rigakafin, yayin da wasu kashi 10 zuwa 15 cikin 100 kuma ba su kammala rigakafin ba. Kaɗan ne kawai daga cikin masu cutar suka kammala samun cikakken rigakafi.
Farfesa Abbas ya ce a halin yanzu tawagarsa na Rano domin binciken mutuwar wasu daga cikin yaran da aka ce sun mutu sakamakon cutar.