’Yan bindiga sun sako yara 48 daga cikin 54 da suka yi garkuwa da su a wani kauye da ke Jihar Neja, bayan an biya kuɗin fansa domin ganin an sake su.
Yaran, wadanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 12, sun shafe kusan makonni uku a hannun ’yan bindigar.
Rahotanni sun ce an sace yaran ne a farkon watan Agusta yayin da suke girbin gyada a wata gona da ke kauyen Sabon Rijiya.
Da farko, gungun ’yan bindiga sun sake yaran a jeji ba tare da an biya fansa ba.
Sai dai yayin da suke kan hanyar komawa gida, wasu ’yan bindigar da ake zargin suna karkashin Dogo Gide sun sake cafke su.
A cewar majiyoyi, an saki yara 40 da dare, sannan aka sake fitar da wasu takwas daga baya.
Sai dai kafin hakan, wata yarinya ta rasu a hannun masu garkuwa da su, yayin da wasu yara biyar suka samu damar tserewa.
Rahotanni sun ce an biya kudin fansa kafin a sako sauran yaran 48.