Akalla mutane 30 ne aka kashe bayan da wasu ‘yan ta’adda suka kai hare-hare kan masallatai hudu a yankin Borgu na Jihar Neja, a lokacin sallar Juma’a.
Rahotanni sun ce maharan sun kai hare-haren ne lokaci guda a Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, inda suka yi awon gaba da sama da mutum 60 zuwa cikin daji. Shugaban Karamar Hukumar Borgu, Mohammed Nasir Abdullahi, ya tabbatar da cewa an kashe kusan 30 daga cikin wadanda aka sace tare da binne gawarwakinsu.
Hare-haren sun kuma haddasa kona wasu gidaje, ciki har da gidan Hakimin Dekara, Abubakar Umar. Bayan lamarin, mazauna yankin da dama sun tsere zuwa New Bussa da Jamhuriyar Benin saboda fargabar sake kai musu hari.
Jami’an tsaro sun kaddamar da samame domin bin sawun maharan da ceto sauran mutanen da ke tsare a hannunsu. Mazauna yankin sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta Jihar Neja su kara yawan jami’an tsaro tare da tallafa wa mutanen da suka rasa muhallansu.
Matsalar tsaro ta shafi akalla unguwanni bakwai cikin 10 na Borgu, inda hare-hare da sace-sace suka tilasta wa dubban manoma barin gidajensu da gonakinsu. Wasu kasuwanni ma sun rufe sakamakon hare-haren, lamarin da ya kara jefa mazauna yankin cikin matsalar tattalin arziki da karancin abinci.