Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn kama dattawa biyu kan zargin yunkurin haikewa yarinya mai shekara 12

An kama dattawa biyu kan zargin yunkurin haikewa yarinya mai shekara 12

’Yan sanda a Calabar, Jihar Cross River, sun kama wasu dattawa biyu, Asuquo Effiom mai shekaru 70 da Moris Monday mai shekaru 68, kan zargin yunkurin yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.

’Yan sanda a Calabar, Jihar Cross River, sun kama wasu dattawa biyu, Asuquo Effiom mai shekaru 70 da Moris Monday mai shekaru 68, kan zargin yunkurin yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.

An kama mutanen ne a ranar Lahadi bayan mahaifin yarinyar ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda. Rahoton ya ce lamarin ya faru ne a yankin Thomas Henshaw da ke Calabar.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce yarinyar ta zargi Monday da yaudararta zuwa dakinsa a ranakun 13 da 14 ga Agusta, inda ta ce ya yi yunkurin lalata da ita.

Ta kuma zargi Effiom da yin irin wannan yunkurin a ranar 22 ga Agusta, bayan ya jawo ta zuwa dakinsa.

’Yan sanda sun ce an samu mutanen ne a hannun wasu mazauna yankin, kafin a mika su ga jami’an tsaro. Sai dai wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.

’Yan sanda sun mika yarinyar zuwa wata cibiyar lafiya da gwamnati ta amince da ita domin duba lafiyarta, yayin da aka tura shari’ar sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments