Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroTallafin Tinubu na İsa ga dukkanin talakawan Najeriya - Gwamnan Sokoto

Tallafin Tinubu na İsa ga dukkanin talakawan Najeriya – Gwamnan Sokoto

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce tasirin manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a rayuwar ’yan Najeriya a bayyane yake, yana mai watsi da ikirarin ’yan adawa cewa gwamnatin tarayya ba ta inganta rayuwar al’umma cikin shekaru uku da suka gabata ba.

Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron yini ɗaya na ƙasa da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya a Jos, Jihar Plateau.

Taron mai taken “Inganta Siyasa da Adalci a Zamantakewa a Matsayin Maganin Haɗin Kai da Ci gaban Najeriya” ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin ƙungiyar.

Gwamnan ya ce ikirarin ’yan adawa cewa babu wani tasirin manufofin Tinubu a rayuwar ’yan Najeriya ba gaskiya ba ne, yana mai cewa irin waɗannan kalamai ba su wuce farfagandar siyasa ba.

A cewarsa, duk wanda yake cewa bai ga tasirin gwamnatin Tinubu a rayuwar ’yan Najeriya ba, to ko dai ba ya Najeriya ko kuma ya bar ƙasar.

Ahmed Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta samar da tallafin abinci da sauran nau’o’in tallafi domin rage wa ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi wahala.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta raba taki kyauta ga manoma tare da samar da wasu tallafe-tallafe da nufin taimaka wa talakawa.

Gwamnan ya ce bai kamata a yi ikirarin cewa gwamnati ba ta tallafa wa talakawa ba, yana mai cewa akwai hujjojin da ke nuna cewa tallafin ya isa ga wasu daga cikin waɗanda ake nufi da shi.

Ya ce:

“Ya kamata mu san cewa abinci ya wadata. Mun san gwamnati ta bayar da taki kyauta. Mun san gwamnati tana bayar da tallafin da ya dace domin taimaka wa talakawa.”

Gwamna Aliyu ya ƙara da cewa ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar suna nan a bayyane, yana mai cewa ’yan Najeriya za su ci gaba da ganin tasirinsu a rayuwarsu.

Ya Bukaci A Sake Zaɓen Tinubu

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi la’akari da sake zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

Aliyu ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Tinubu ba zai ba Najeriya kunya ba, yana mai cewa ya kamata al’umma su duba ayyukan da gwamnatin ta gudanar kafin yanke hukunci.

Taron ya samu halartar Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf; Gwamnan Jigawa, Umar Namadi; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da sauran manyan baki.

Sai dai ’yan adawa sun yi watsi da iƙirarin da gwamnatin Tinubu da magoya bayanta ke yi kan nasarorin da ta samu, musamman a fannin tattalin arziki, inda suke ci gaba da bayyana damuwarsu kan halin da ’yan Najeriya ke ciki.

A wani ɓangare na ayyukan gwamnatin Sokoto kuwa, Gwamna Ahmed Aliyu ya raba motoci 62 na yaƙi da kayan aikin tsaro ga jami’an tsaron da ke aiki a jihar, ƙarƙashin shirin Operation Fight Terrorism, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata ta’addanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments