Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaBa cire tallafin mai Tinubu ya yi ba, ya bai wa abokansa...

Ba cire tallafin mai Tinubu ya yi ba, ya bai wa abokansa dukiyar kasa – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin abin da ya kira nuku-nuku kan batun cire tallafin man fetur.

Atiku ya ce gwamnati ba za ta ce ta kawo ƙarshen tallafin man fetur ba, alhali tana bai wa masu zuba jari a harkar man fetur rangwamen haraji, tallafin kuɗi da sauran gata na musamman.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, Atiku ya bayyana bikin da gwamnatin Tinubu ke yi kan cire tallafin man fetur a matsayin “ɗaya daga cikin manyan yaudarar tattalin arziki” da ake yi wa ’yan Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce yayin da talakawa ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin man fetur, sufuri da kayan abinci, gwamnati na rage wa manyan masu zuba jari a masana’antar man fetur haɗarin kasuwanci ta hanyar ba su rangwamen haraji da sauran tallafe-tallafe.

Atiku ya yi zargin cewa abin da ake kira cire tallafin man fetur bai kawo ƙarshen dukkan nau’o’in tallafin da gwamnati ke bayarwa a ɓangaren makamashi ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta bayyana wa ’yan Najeriya a fili irin kuɗaɗen da take kashewa da kuma waɗanda ke amfana da irin waɗannan shirye-shirye.

Atiku ya kuma yi nuni da bayanan asusun Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC), inda ya ce an kashe kusan Naira tiriliyan 4.84 a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 7.13 a shekarar 2024 kan abubuwan da aka bayyana da suna “energy security” da kuma sauran gibin farashin man fetur.

Ya ce ya kamata a yi cikakken bayani kan yadda waɗannan kuɗaɗe suka fita da kuma irin tasirin da suka yi ga rayuwar ’yan Najeriya.

Atiku ya ƙara da cewa matsalar ba wai kawai batun cire tallafin man fetur ba ce, illa yadda ake gudanar da tsarin da kuma yadda nauyin manufofin gwamnati ke sauka kan talakawa.

Ya ce yayin da ’yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, gwamnati na buƙatar samar da tsare-tsaren da za su rage musu radadin hauhawar farashin man fetur da sauran kayayyakin masarufi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya buƙaci gwamnatin tarayya ta kasance mai gaskiya da bayyana gaskiya wajen gudanar da harkokin man fetur da sauran albarkatun ƙasa.

Sai dai zarge-zargen Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke kare manufofinta na cire tallafin man fetur, tana mai cewa sauyin ya zama dole domin rage nauyin da tallafin ke ɗora wa kuɗin gwamnati da kuma samar da damar saka hannun jari a sauran sassan tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments