Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroSojojin sama sun kashe mayakan ISWAP, sun lalata motocin yaƙi biyu a...

Sojojin sama sun kashe mayakan ISWAP, sun lalata motocin yaƙi biyu a Borno

Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ta gudanar da hare-haren sama kan mayakan ƙungiyar ISWAP a ƙauyen Aduwa, Ƙaramar Hukumar Guzamala ta Jihar Borno.

Rahotanni sun ce hare-haren, waɗanda aka kai ranar 21 ga Agusta, 2026, sun hallaka wasu mayakan ISWAP tare da lalata motocin yaƙi guda biyu na ƙungiyar.

A cewar Zagazola Makama, wata kafar da ke bibiyar harkokin tsaro da yaƙi da ta’addanci, bayanan sirri sun nuna cewa harin ya yi matuƙar tasiri.

Rahoton ya ce dukkan mutanen da aka gani a yankin da aka kai harin an tantance su a matsayin mayakan ISWAP.

Ɗaya daga cikin motocin yaƙin da aka kai wa harin ta kone kurmus sakamakon farmakin, yayin da aka lalata ɗayar.

Bayan harin, an ga wasu daga cikin mayakan da suka tsira suna ƙoƙarin kwashe abokan aikinsu da suka jikkata daga yankin.

Wasu daga cikinsu kuma sun yi ƙoƙarin jan wata motar yaƙi da ta lalace zuwa wajen Gudumbali, da alama suna kan hanyar zuwa yankin Tafkin Chadi.

Rahoton ya ce wannan yunƙuri na daga cikin matakan da mayakan da suka tsira ke ɗauka domin ceto waɗanda suka jikkata da kuma ficewa daga yankin da aka kai harin.

Harin na zuwa ne yayin da rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da gudanar da hare-haren sama da na ƙasa domin dakile ayyukan ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments