Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Ƙasa (JAMB) ta ƙaddamar da sabon tsarin da zai bai wa ɗalibai damar tantancewa da loda sakamakon O’Level daga gidajensu, ba tare da zuwa cibiyoyin CBT ba.
JAMB ta ce an haɗa tsarin e-Facility da bayanan hukumomin da ke gudanar da jarabawar, domin a tantance sahihancin sakamakon kafin a loda shi cikin bayanan ɗan takara.
Hukumar ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinta na amfani da fasaha wajen rage cunkoso, layuka da yawan zuwa cibiyoyin CBT domin gudanar da ayyukan da za a iya kammalawa ta yanar gizo.
‘Yan takarar da ke da sakamakon O’Level guda biyu za su shiga shafin e-Facility, su zaɓi “2026 UTME O’Level Upload”, sannan su shigar da bayanan da ake buƙata domin tabbatar da sakamakonsu.
Bayan an tabbatar da sakamakon, JAMB za ta bai wa ɗan takarar Verification Code, wanda zai aika ta saƙon SMS zuwa 55019 ko 66019 kafin a kammala aikin loda sakamakon.