Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAPC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har bayan 2031...

APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har bayan 2031 –Yari

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, Sanata Abdul’Aziz Yari, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulkin Najeriya har bayan shekarar 2031.

Yari ya bayyana hakan ne a Abuja bayan dawowarsa daga ƙasar waje, inda magoya bayan jam’iyyar APC suka tarbe shi.

Sanatan ya ce APC na da cikakken yaƙinin samun nasara a zaɓen 2027, bisa la’akari da abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.

A cewarsa, ayyukan da gwamnatin ta gudanar da kuma manufofin da ta aiwatar za su taimaka wajen ƙara wa jam’iyyar ƙarfi da samun goyon bayan ’yan Najeriya a zaɓen da ke tafe.

Yari ya kuma yi kira ga mambobin APC da su haɗa kai tare da mayar da hankali wajen ganin an samu nasarar sake zaɓen Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu.

Sai dai nadin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu ya jawo suka daga wasu ɓangarori, musamman kan shigar da wasu jami’an gwamnati da kuma mutanen da ake fuskantar zarge-zargen da suka shafi rashin gaskiya da kuɗi.

Duk da sukar da ake yi, Yari ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatin APC za ta ci gaba da ƙoƙarin cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin zaɓen 2023.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya bai wa Shugaba Tinubu hikima da basirar da za su taimaka masa wajen jagorantar ƙasar.

Yari ya bayyana fatan cewa APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta jagoranci Najeriya har bayan wa’adin mulkin Tinubu na biyu, yana mai cewa jam’iyyar na da shirin ci gaba da samun goyon bayan al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments