Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiShugaban APC ya fadi ya mutu yayin taron sulhu a Kogi

Shugaban APC ya fadi ya mutu yayin taron sulhu a Kogi

Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, Oyewole Mayowa Solomon, ya rasu bayan ya faɗi a yayin wani taron sulhu da aka gudanar a garin Iyara.

Rahotanni sun ce Solomon ya faɗi ne a ranar Juma’a yayin da ake gudanar da taron.

An dai ba shi agajin gaggawa kafin daga bisani aka garzaya da shi wani asibiti a Kabba, inda aka tabbatar da rasuwarsa bayan isa asibitin.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijumu, Funsho Olumoko, ne ya shirya taron da nufin sasanta rikicin cikin gida tsakanin ɓangarorin jam’iyyar APC tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta.

An gudanar da taron ne domin haɗa shugabannin siyasa, shugabannin jam’iyya na ƙaramar hukuma da mazabu, shugabannin mata da matasa, da kuma waɗanda gwamnati ta naɗa daga mazabu 15 na Ijumu.

Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi ta Yamma, da Hon. Salman Idris, mai wakiltar mazabar Kabba-Bunu/Ijumu a Majalisar Wakilai, sun bayyana alhininsu kan rasuwar Solomon.

Sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai biyayya, jajircewa da kuma ƙwarewa wajen haɗa kan jama’a, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa, ƙaramar hukumar Ijumu da jam’iyyar APC baki ɗaya.

A lokacin tattara rahoton, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, bai mayar da martani kan tambayar da aka aika masa game da lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments