Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi alkawarin bayar da tallafin Naira miliyan 600 domin gina ɗakin kwanan ɗalibai mata a Jami’ar Jihar Lagos (LASU).
Dangote ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai na karo na 29 da 30 da jami’ar ta gudanar a babban harabarta da ke Ojo, jihar Lagos.
Haka kuma, attajirin ya yi alkawarin bai wa ɗaliban LASU da suka kammala karatun digiri na farko a fannonin Injiniya da Kimiyya fifiko wajen samun aikin yi a kamfaninsa bayan kammala bautar ƙasa ta NYSC.
An bayyana cewa Rukunin Kamfanonin Dangote na ɗaukar ma’aikata sama da 52,000 a Najeriya da wasu ƙasashe 11 na Afirka, yayin da Dangote Academy ke bayar da horo ga matasa da waɗanda suka kammala karatu.
A yayin bikin, Aliko Dangote ya samu lambar girmamawa ta digirin digirgir a fannin kasuwanci, bunƙasa masana’antu da jari na ɗan Adam. ‘Yarsa, Fatima Aliko Dangote, ce ta wakilce shi wajen karɓar lambar.
Bikin ya kuma samu tallafin Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, inda ya bai wa ɗalibai biyu da suka fi fice Naira miliyan 20 kowanne.
A cewar jami’ar, LASU ta samar da waɗanda suka kammala karatu 20,604 a shekarun karatu na 2024/2025 da 2025/2026.