Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya taya Maryam Ibrahim Dan’azumi daga jihar Gombe murnar lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa karo na 46 da aka gudanar a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Maryam ta wakilci Najeriya a gasar Sarki Abdulaziz, inda ta zama zakara a ɓangaren mata na haddar Alƙur’ani mai girma, karatu da Tajwidi da kuma Tafsiri na Izu 60.
A cikin wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana nasarar Maryam a matsayin babban abin alfahari ga Najeriya da daukacin al’ummar Musulmi.
Sarkin Musulmi ya ce nasarar ta nuna irin hazaka da damar da matasan Najeriya suke da ita idan aka ba su ingantaccen ilimi, kulawa da jagoranci.
Ya kuma jaddada muhimmancin bai wa ’ya’ya mata dama da tallafi domin su cimma manyan nasarori a rayuwarsu.
A cewar sanarwar, gasar ta bana ta kasance ta musamman, kasancewar ita ce karo na farko da aka bai wa mata damar shiga gasar tun bayan shafe shekaru 46 ana gudanar da ita.
Sarkin Musulmi ya ce abin farin ciki ne yadda Maryam, ’yar Najeriya, ta samu nasarar daga tutar ƙasar a irin wannan gasa ta duniya.
Nasarar Maryam ta ƙara zuwa cikin jerin nasarorin da matasan Najeriya ke samu a duniya, ciki har da Nafisa Aminu, wadda ta lashe gasar TeenEagle a London a shekarar 2025.
Haka kuma, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam murnar wannan gagarumar nasara, bayan da ta doke mahalarta daga ƙasashe 132 tare da lashe kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya.