Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a Jihar Sokoto ta gargadi gwamnatin jihar kan yiwuwar kai hare-hare da sace mutane a jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.
Rahotanni sun ce hukumar ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga na shirin kai hare-hare kan cibiyoyin ilimi da ke jihar.
DSS ta ce akwai alamun cewa ‘yan ta’addan sun fara sauya salon hare-harensu, inda ake zargin sun karkata daga makarantun firamare da sakandare zuwa manyan makarantun gaba da sakandare.
Gargadin na kunshe ne cikin wata wasika da ofishin DSS na Jihar Sokoto ya aikewa gwamnatin jihar a ranar 18 ga Yuli, 2026.
Hukumar ta bukaci gwamnatin jihar da hukumomin da abin ya shafa su dauki matakan tsaro da suka dace domin kare rayukan dalibai, malamai da sauran ma’aikatan manyan makarantun jihar.