Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiAn yi jana’izar mutane 52 bayan hatsarin kwale-kwale a Sokoto

An yi jana’izar mutane 52 bayan hatsarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutane 52 ne aka yi wa jana’iza a jihar Sokoto bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da manoma da ma’aikata ya kife a Gorau, ƙaramar hukumar Goronyo.

Lamarin ya faru ne a safiyar Laraba, lokacin da kwale-kwalen ke ƙoƙarin tsallaka wani kogi domin kai mutanen zuwa gonakinsu na shinkafa.

Rahotanni sun ce sama da mutane 60 ne ke cikin kwale-kwalen a lokacin da ya kife, ciki har da mata da ƙananan yara.

Shugaban ayyuka na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) a Sokoto, Alhaji Tukur Abubakar, ya ce har yanzu ba a tabbatar da cikakken adadin mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba.

Sai dai ya tabbatar da cewa an tsamo gawawwakin mutane 52 daga cikin ruwan, kuma an yi jana’izarsu.

Daga cikin waɗanda suka rasu har da mutane 11 daga iyali guda, lamarin da ya ƙara jefa al’ummar yankin cikin alhini da jimami.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments