Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShettima: Tinubu na samar da damammaki a faɗin Najeriya

Shettima: Tinubu na samar da damammaki a faɗin Najeriya

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da samar da damammaki da ayyukan more rayuwa a sassa daban-daban na Najeriya.

Shettima ya ce zuba jari a ayyukan more rayuwa na da muhimmiyar rawa wajen rage cunkoso, samar da guraben ayyukan yi da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziki.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake wakiltar Shugaba Tinubu wajen kaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 33.5 a Jihar Rivers.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya ce irin wadannan ayyuka na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin inganta sufuri da tallafa wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments