Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaTinubu ya gana da gwamnan Osun, Adeleke, a fadar shugaban kasa

Tinubu ya gana da gwamnan Osun, Adeleke, a fadar shugaban kasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Adeleke ya isa fadar Aso Rock da misalin ƙarfe 5:25 na yamma, kwanaki kaɗan bayan samun nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar.

Wannan dai shi ne karon farko da gwamnan ya gana da Shugaba Tinubu tun bayan sake zaɓensa.

Gwamnan ya samu rakiyar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu manyan jami’an gwamnatin Jihar Osun.

Daga cikin waɗanda suka raka shi akwai Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Sanata Lere Oyewumi, da Shugaban Ma’aikatan Gwamnan, Akinleye Kazeem.

Ganawar ta zo ne bayan da Shugaba Tinubu ya kira Adeleke ta waya domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaɓen.

Ana sa ran fadar shugaban ƙasa za ta fitar da ƙarin bayani kan batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments