Ana fargabar mutuwar kusan mutane 40 bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da manoma da ma’aikatan aikin gona ya kife a garin Gorau, da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce kwale-kwalen na ɗauke da sama da mutane 70, ciki har da yara masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15, lokacin da ya kife jim kaɗan bayan ya taso domin tsallaka wani rafi zuwa gonakin shinkafa.
An ce shugaban ƙauyen na cikin waɗanda suka shiga kwale-kwalen, amma daga baya aka samu nasarar ceto shi tare da wasu mutane.
Wani ɗan jarida da ya kasance a wurin, Sharhabilu Yahuza Kiliya, ya ce zuwa yanzu an gano gawarwakin kusan mutane 40, yayin da aka ceto mutum shida.
Ana ci gaba da aikin ceto da neman wadanda har yanzu ba a san inda suke ba, tare da kokarin gano sauran gawarwakin.