Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaBai kamata a hada siyasa da rigingimun addini a Najeriya ba –...

Bai kamata a hada siyasa da rigingimun addini a Najeriya ba – Sheikh Daurawa

Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce bai kamata a hada siyasa da rigingimun addini a Najeriya ba, yana mai cewa ’yan kasa su zabi shugabanni bisa kwarewa da irin ayyukan da suke da niyyar yi wa al’umma.

Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da DW Hausa, inda ya yi bayani kan batun tikitin Musulmi da Musulmi da kuma sauran tsarin hadin kan ’yan takara a zaben Najeriya.

Malamin ya ce siyasa ba addini ba ce, don haka bai kamata a rika amfani da bambancin addini wajen zagi, cin mutunci ko kafirta mutane saboda ra’ayinsu na siyasa ba.

A cewarsa, tikitin Musulmi da Musulmi, Musulmi da Kirista ko kuma Kirista da Kirista duk hanyoyi ne na siyasa, kuma bai kamata a mayar da su wata hanyar rarrabuwar kan al’umma ba.

Sheikh Daurawa ya ce abin da ya kamata ’yan Najeriya su fi mayar da hankali a kai shi ne abin da dan takara zai iya yi idan aka ba shi mulki, maimakon la’akari da addinin wanda yake tare da shi.

Ya kuma jaddada cewa babu wata jam’iyyar siyasa da za a kira ta jam’iyyar Musulunci ko Kiristanci, don haka bai kamata a mayar da bambancin addini babban makamin yakin neman zabe ba.

Malamin ya ce duk wanda ya goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi ko kuma wanda ya fifita wani tsarin hadin kai na daban bai kamata a zarge shi da laifin addini ba, muddin yana bayyana ra’ayinsa cikin mutunci.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su daina kallon siyasa a matsayin rigimar addini, su mayar da hankali kan shugabanci nagari, kwarewa, gaskiya da kuma amfanin da al’umma za ta samu daga wanda za ta zaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments