Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dauki sabon mataki domin karfafa tsaron kasa, inda ya amince da fara gudanar da cikakken bincike kan barazanar tsaro da kuma tsara sabon shirin dabarun tsaro na shekaru biyar.
Tinubu ya kafa kwamitin mutum 11 da zai jagoranci aikin, karkashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaron Cikin Gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa.
An bayar da wa’adin kwanaki 90 ga kwamitin domin kammala binciken da tsara shirin, sannan ya gabatar da rahoton ga Shugaban Kasa domin duba shi da kuma amincewa.
Matakin na daga cikin kokarin gwamnati na inganta hadin gwiwa tsakanin sojoji, hukumomin tsaro da sauran hukumomin leken asiri wajen tunkarar sauye-sauyen barazanar da Najeriya ke fuskanta.
Daga cikin wadanda ke cikin kwamitin akwai Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; da Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle.
Sauran mambobin sun hada da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede; shugabannin rundunonin Sojin Kasa, Sama da Ruwa, da kuma shugabannin hukumomin DSS da NIA.
Shugaban Kasa ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen samar da fahimta guda kan matsalolin tsaron kasar, manufofin da ya kamata a cimma da kuma irin karfin da ake bukata domin tunkarar barazanar.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, yana mai cewa wasu daga cikin nasarorin baya-bayan nan wajen ceto mutanen da aka sace sun nuna amfanin aiki tare tsakanin hukumomin tsaro da na leken asiri.
Kwamitin ya fara aiki nan take, kuma ana sa ran zai kammala Binciken Barazanar Tsaron Kasa da Shirin Dabarun Ayyukan Tsaro na shekaru biyar cikin kwanaki 90.