Dan fafutukar kare hakkin bil’adama kuma dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, ya soki NDLEA kan lalata gonakin tabar wiwi a Jihar Edo.
Sowore ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta halatta noman tabar wiwi tare da tsara yadda za a gudanar da shi, yana mai cewa hakan na iya samar da damar tattalin arziki, ayyukan yi da kuma bunkasa bincike.
Ya ce lalata gonakin da ake zargin suna da darajar miliyoyin daloli ba zai magance matsalar talauci a Najeriya ba.
Sai dai NDLEA ta ce ta lalata gonakin tabar wiwi guda biyu a Edo, wadanda aka kiyasta za su samar da kimanin kilogram 4,628.9 na tabar wiwi.
Hukumar ta kuma ce ta kama mutane 10 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a wasu samame da ta gudanar a jihar, inda aka kwato tabar wiwi da wasu nau’ikan kwayoyi.
Kwamandan NDLEA na Edo, Mitchell Ofoyeju, ya ce an kama wadanda ake zargin ne bisa sahihan bayanan sirri, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.