Gwamnatin Kano ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Gidauniyar Dangote domin miƙa mata Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Dangote na tsawon shekaru 20.
Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya ce haɗin gwiwar zai bai wa matasa damar koyon sana’o’in hannu da dabarun fasaha domin dogaro da kansu.
Ya ce cibiyar za ta kuma samar da damar koyon dabarun kasuwanci, wanda zai taimaka wa matasa wajen kafa sana’o’insu da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin jihar.
Umar Farouk ya bayyana miƙa cibiyar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na rage rashin aikin yi da samar da hanyoyin dogaro da kai masu ɗorewa ga al’ummar Kano.
A nata ɓangaren, Gidauniyar Dangote ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa ilimi, koyar da sana’o’i da ƙarfafa tattalin arziki, musamman tsakanin matasa.