Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayar da umarnin rushe gidajen da aka gano suna toshe hanyoyin magudanan ruwa a Maitama da wasu yankunan babban birnin tarayya da ke fuskantar barazanar ambaliya.
Wike ya bayar da umarnin ne a ranar Talata bayan duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama.
Ya ce aikin rushe-rushen zai fara nan take, kuma zai ci gaba har zuwa ranar Asabar, ba tare da la’akari da siyasa ko matsayin masu mallakar gine-ginen ba.
A cewarsa, matakin na da nufin cire duk wani abu da ke kawo cikas ga kwararar ruwa tare da rage yiwuwar sake samun ambaliya an Abuja.