Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan al’ummomi da dama a Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.
Mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye ƙauyuka akalla shida da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe.
An ce harin ya shafi Ayaba, Ukpen, Bom, Ikpur, Aboajio da Yina, duk a gundumar Mbaterem ta Ukum. Shaidu sun ce maharan sun zo ne da babura da dama.
An kuma samu rahoton raunata wasu mutane da harsasai, yayin da mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ukum, Jonathan Modi, ya ce jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa tare da shawo kan lamarin.
Ya ce a lokacin da yake magana, yana wurin da aka kai harin, inda ake kwashe gawawwaki da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Rundunar ’yan sandan jihar ma ta tabbatar da harin, inda kakakinta, Peter Aondongu, ya ce ana ci gaba da tattara cikakkun bayanai kan lamarin.
Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da yabawa jami’an tsaro bisa gaggawar da suka yi ta mayar da martani.
Alia ya zargi wasu makiyaya masu ɗauke da makamai da hannu a harin, tare da tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kasance cikin taka-tsantsan tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani motsi na mutane ko abubuwan da ake zargi.