Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmbaliyar ruwa ta katse hanyoyi a Abuja, ta jefa masu ababen hawa...

Ambaliyar ruwa ta katse hanyoyi a Abuja, ta jefa masu ababen hawa cikin wani yanayi

Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Abuja ranar Asabar, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirga tare da tilasta wasu ‘yan kasuwa rufe wuraren sana’arsu.

Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Abuja ranar Asabar, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirga tare da tilasta wasu ‘yan kasuwa rufe wuraren sana’arsu.

Daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa akwai Adetokunbo Ademola Crescent da ke Wuse 2, yankin Delight Event Centre a Gudu da wasu sassan Efab Estate da ke Lokogoma.

Gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi ma ta cika da ruwa, lamarin da ya hana masu ababen hawa wucewa cikin sauƙi. Wasu motoci sun nutse ko suka samu matsala sakamakon hauhawar ruwan.

Wani mazaunin yankin Ebeano-Gudu ya yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, da ya gaggauta ɗaukar mataki domin magance matsalar.

Ya ce ambaliyar ta katse hanyar da ke tsakanin Ebeano da Gudu, inda mazauna da masu ababen hawa suka koma neman wasu hanyoyin bi.

Lamarin ya sake haifar da tambayoyi kan ingancin matakan da ake ɗauka wajen hana ambaliyar ruwa da kuma tsarin magudanan ruwa a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa sama da Naira biliyan 109.5 aka fitar daga Asusun Muhalli na Najeriya tsakanin Yulin 2023 da Disamban 2025 domin tunkarar matsalolin muhalli, musamman ambaliyar ruwa.

Sai dai duk da waɗannan kuɗaɗe, ambaliyar na ci gaba da janyo asarar dukiya da kawo cikas ga zirga-zirga a sassan Abuja.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) da Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa (NIHSA) sun yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a lokacin daminar bana, musamman tsakanin watannin Agusta da Satumba.

An kuma sanya Abuja cikin yankunan da ke fuskantar babban haɗarin ambaliyar ruwa, musamman ambaliyar gaggawa da ka iya faruwa sakamakon ruwan sama mai ƙarfi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments