Babban Bishop na Cocin Katolika na Maiduguri, Oliver Dashe, ya yi kira ga Kiristoci da su ƙara yawaita addu’a domin kawo ƙarshen matsalar tsaro, musamman Boko Haram.
Bishop Dashe ya bayyana hakan a Maiduguri yayin bikin Solemnity of the Assumption of the Blessed Virgin Mary, inda ya ce addu’a kaɗai ba ta isa ba, sai gwamnati da jami’an tsaro sun ɗauki matakan da suka dace.
Ya ce duk da samun ɗan sauƙin tsaro a wasu sassan Borno, bai kamata jama’a su yi sakaci ba. Ya kuma yi kira ga gwamnati ta bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya domin kai samame a dazuzzuka da tsaunukan da ’yan ta’adda ke fakewa.
Bishop ɗin ya ce samun sauƙin tsaro ya ba wasu mutanen da suka tsere daga gidajensu a lokacin rikicin damar komawa garuruwansu.
Ya ƙara da cewa dorewar zaman lafiya na buƙatar haɗin gwiwar jama’a, gwamnati da jami’an tsaro wajen dakile ragowar ’yan ta’addan.