’Yan bindiga 17 da ’yan sanda 10 sun mutu yayin wata arangama tsakanin jami’an tsaro da wasu ’yan bindiga a yankin Rafin Makuku, da ke Ƙaramar Hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi.
Rundunar ’Yan Sandan Kebbi ta ce lamarin ya faru ne a safiyar Litinin, lokacin da jami’anta suka tare ’yan bindigar da ke ƙoƙarin tsallakawa daga Zamfara zuwa Kebbi dauke da muggan makamai.
Kakakin rundunar, DSP Bashir Usman, ya ce an kashe ’yan bindiga 17 tare da ƙona babura huɗu a yayin arangamar. Ya ƙara da cewa ’yan sanda 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata.
Rundunar ta kuma tabbatar da mutuwar fararen hula biyu a yayin musayar wutar. Sai dai wani mazaunin yankin ya yi zargin cewa ’yan bindigar sun kwashe wasu bindigogin jami’an da suka kashe.
Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kai kimanin 240, da ke amfani da babura sama da 200, inda ake zargin sun fito ne daga yankin Sangeko Gap na Ƙaramar Hukumar Maru a Zamfara.
Kakakin ’yan sandan ya ce rundunar na ci gaba da tattara bayanai kan adadin waɗanda suka mutu da suka jikkata, tare da gudanar da samame domin cafke ’yan bindigar da suka tsere.
Ya kuma bayyana jami’an da aka kashe a matsayin gwaraza da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma, yana mai cewa rundunar za ta tallafa wa iyalansu tare da kula da jami’an da suka jikkata.