Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojoji sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a...

Sojoji sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a Kogi

Rundunar Sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Ruwa, ’yan sanda, ’yan banga da mafarauta sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi.

Rundunar Sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Ruwa, ’yan sanda, ’yan banga da mafarauta sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi.

An yi garkuwa da mutanen ne ranar Lahadi, 9 ga Agusta, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan matafiya a hanyoyin Ojuwo–Ajengo–Memarebo da Ojiwo–Itobe, a Ƙaramar Hukumar Ofu.

Bayan samun bayanan sirri cewa masu garkuwar sun tafi da mutanen zuwa yankin Adumu a Ƙaramar Hukumar Dekina, dakarun Bataliya ta 21 da jami’an NNS Lugard suka fara aikin ceto tare da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro.

A yayin aikin, jami’an tsaron sun yi musayar wuta da masu garkuwar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji. Daga bisani jami’an tsaron suka ceto dukkan mutanen 16 da aka yi garkuwa da su.

Daga cikin waɗanda aka ceto akwai maza shida, mata shida da yara huɗu. A halin yanzu suna samun kulawar likitoci yayin da ake kammala shirye-shiryen mayar da su ga iyalansu.

Sai dai wani mafarauci ya rasa ransa yayin aikin, yayin da wani ɗan sanda ya samu rauni kuma yake karɓar magani. Rundunar Sojojin Najeriya ta yaba da gudunmawar jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da garkuwa da mutane.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments