Zanga-zangar Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen sama a Legas ranar Talata, lamarin da ya sa fasinjojin Air Peace suka makale a filin jirgin sama.
Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 5 na Asuba, inda aka rufe ƙofar tashar Zulu Terminal. Hakan ya hana jirgin Air Peace da aka shirya tashi da ƙarfe 6:30 na safe barin Legas.
Lamarin ya jawo ɓacin rai tsakanin fasinjojin da abin ya shafa, yayin da wasu suka ce rashin samun cikakken bayani kan lokacin da za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen ya dagula musu tsare-tsaren tafiya.
Wani ma’aikacin Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ƙi bayyana dalilin zanga-zangar. Sai dai wani ma’aikacin harkokin jiragen sama ya ce zanga-zangar na da alaƙa da ƙoƙarin tabbatar da haƙƙin ma’aikatan Air Peace na shiga ƙungiyar ƙwadago.
Ƙoƙarin tuntuɓar kamfanin Air Peace domin samun ƙarin bayani bai yi nasara ba, yayin da fasinjojin da suka makale ke ci gaba da jiran bayani kan lokacin da za a dawo da zirga-zirgar jiragen.