Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanci’Yan Najeriya sun sha datar Naira tiriliyan 6.6 a shekara guda

’Yan Najeriya sun sha datar Naira tiriliyan 6.6 a shekara guda

’Yan Nijeriya sun kashe kimanin naira tiriliyan 6.6 wajen sayen data cikin watanni 12 da suka gabata, lamarin da ke nuna yadda amfani da intanet ke ƙara bunƙasa a ƙasar.

’Yan Nijeriya sun kashe kimanin naira tiriliyan 6.6 wajen sayen data cikin watanni 12 da suka gabata, lamarin da ke nuna yadda amfani da intanet ke ƙara bunƙasa a ƙasar.

An ƙididdige adadin ne bisa bayanan Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) kan yawan amfani da intanet, tare da amfani da matsakaicin farashin naira 431 kan kowane gigabyte (GB). Ba wai bisa bayanan kuɗaɗen shiga da kamfanonin sadarwa suka bayyana ba.

Bayanan NCC sun nuna cewa an yi amfani da terabytes miliyan 15.32 na data tsakanin Yunin 2025 da Mayun 2026. Wannan ya yi daidai da kusan GB biliyan 15.32, wanda idan aka ninka da naira 431 ya kai kusan naira tiriliyan 6.6.

Kafin ƙarin kuɗin sadarwa na kashi 50 da NCC ta amince da shi a Janairun 2025, matsakaicin farashin 1GB na data ya kai kusan naira 287.50. Bayan ƙarin kuɗin da ya fara aiki a Fabrairu, farashin ya tashi zuwa kusan naira 431.25, yayin da farashin kasuwa ya kasance tsakanin naira 475 da naira 637.50, gwargwadon kamfani da kunshin data.

NCC ta kuma nuna cewa amfani da data a kowane wata ya ƙaru daga terabytes miliyan 1.04 a Yunin 2025 zuwa terabytes miliyan 1.50 a Mayun 2026, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 44 cikin 100.

Amfani da intanet ɗin ya haɗa da layukan kamfanonin sadarwa da dama, da suka haɗa da GSM, masu samar da sabis na intanet (ISP), layukan intanet na waya da sauran fasahohin sadarwa. Sai dai NCC ta yi bayanin cewa farashin naira 431 da aka yi amfani da shi wajen ƙididdigar matsakaici ne, domin a zahiri farashin data ya bambanta bisa kamfani, kunshi da sauran sharuddan kasuwanci.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments