Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMummunan hatsari ya hallaka sojoji 17 da wasu mutane 5 a Nijar

Mummunan hatsari ya hallaka sojoji 17 da wasu mutane 5 a Nijar

Mutum 22 sun rasa rayukansu, ciki har da sojoji 17, yayin da wasu 37 suka samu raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Maradi zuwa Madaoua, a jihar Tahou ta Jamhuriyar Nijar.

Mutum 22 sun rasa rayukansu, ciki har da sojoji 17, yayin da wasu 37 suka samu raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Maradi zuwa Madaoua, a jihar Tahou ta Jamhuriyar Nijar.

Hatsarin ya faru ne ranar Juma’a da misalin ƙarfe 8:00 na safe, lokacin da wata motar bas ta kamfanin STM da ke tafiya daga Madaoua ta yi taho-mu-gama da wata bas ta kamfanin SONITRAV da ke zuwa daga Zinder, wadda ke ɗauke da jami’an sojoji da suka kammala horo.

Rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Nijar (ANP) ya ce mutum 22 sun mutu nan take a hatsarin, yayin da mutum 37 suka samu raunuka daban-daban. Ba a bayyana cikakken bayani kan halin da waɗanda suka jikkata ke ciki ba.

Ministan Sufuri na Nijar, Kanal-Manjo Abdourahamane Amadou, ya ce zai gayyaci kamfanonin STM da SONITRAV zuwa ofishinsa ranar Litinin domin neman ƙarin bayani kan musabbabin hatsarin da kuma matakan da suka ɗauka.

Ma’aikatar Sufurin ta jaddada cewa nauyin tabbatar da tsaro da lafiyar fasinjoji yana kan kamfanonin sufuri, inda ta bukace su da su riƙa kula da motocinsu akai-akai, bin dokokin tuƙi da kuma tabbatar da direbobi suna samun isasshen lokacin hutu.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments