Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojoji sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da...

Sojoji sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Zamfara

Dakarun haɗin gwiwar Operation FANSAN YAMMA sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yankin Magazu da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Dakarun haɗin gwiwar Operation FANSAN YAMMA sun ceto fasinjoji 33 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yankin Magazu da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

An ceto mutanen ne ranar Asabar, bayan dakarun sun samu sahihin bayanin sirri cewa ’yan ta’addan sun tare matafiya tare da yin garkuwa da su yayin da suke wucewa ta yankin.

Mai ba da bayanai kan ayyukan yaƙi na rundunar Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce dakarun sun haɗa kai da jami’an ’yan sanda da aka girke a Tsafe wajen kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton.

Ya ce jami’an sun yi arba da ’yan ta’addan ne yayin da suke ƙoƙarin kai fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba, inda suka buɗe musu wuta. Hakan ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa zuwa dazuzzukan da ke kusa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Dakarun sun tabbatar da ceto dukkan fasinjojin 33 ba tare da wani daga cikinsu ya rasa rai ba, sannan suka fara farautar ’yan ta’addan da suka tsere.

Kwamandan Operation FANSAN YAMMA ya yaba wa dakarun bisa gaggawar da suka yi da kuma ƙwarewar da suka nuna, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da kare fararen hula da kuma tabbatar da tsaron manyan hanyoyin sufuri a Arewa maso Yamma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments