Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKano: Mutumin da ya rasa mata da ’ya’yansa shida ya sake yin...

Kano: Mutumin da ya rasa mata da ’ya’yansa shida ya sake yin aure a shirin auren gata

Malam Haruna Bashir, wanda ya yi rashin matarsa da ’ya’yansa shida sakamakon wani mummunan lamari, ya samu damar fara sabuwar rayuwa bayan ya shiga cikin shirin Auren Gata na Gwamnatin Jihar Kano.

Haruna Bashir ya kasance cikin waɗanda suka amfana da shirin, inda ya sake yin aure tare da fara sabon babi na rayuwarsa bayan babban rashi da ya fuskanta.

A wani mataki na tallafa masa, Gwamnan Jihar Kano ya kuma ba shi kyautar gida a Kwankwasiyya City, domin taimaka masa wajen sake gina rayuwarsa da samun kwanciyar hankali.

Shirin ya ba Haruna damar samun sabon abokin rayuwa da kuma damar farfaɗo da rayuwarsa bayan mummunan al’amarin da ya yi sanadin rasa iyalansa shida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments