Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, SFIPMA, MNIM, MNIPS, MASIS, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Karaye (Kyauran Yammawa), Alhaji Dr. Muhammad Maharaz, a fadarsa da ke Karaye.
Ziyarar ta yi daidai da umarnin Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, psc(+), NPM, na ci gaba da ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da al’umma ta hanyar tsarin Community Policing, domin ƙara amincewa, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin rundunar ’yan sanda da jama’a.
Yayin ziyarar, Kwamishinan ’Yan Sandan ya gode wa Mai Martaba Sarkin bisa irin goyon bayan da yake bai wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, da kuma shawarwarin tsaro da yake bayarwa.
Ya yaba da rawar da Sarkin ke takawa wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da al’umma a Karaye da ƙananan hukumomin da ke makwabtaka da yankin, wanda ya ce ya taimaka matuƙa wajen samar da zaman lafiya a masarautar.
Kwamishinan ya jaddada cewa sarakunan gargajiya su ne ginshiƙai da masu kula da tsarin Community Policing a yankunansu.
Don haka, ya yi kira ga cibiyar gargajiya da ta ci gaba da bai wa ’yan sanda goyon baya, haɗin kai, addu’a da ƙarfafawa, domin su samu damar gudanar da aikin kare rayuka da dukiyoyin jama’a yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Muhammad Maharaz, ya gode wa Kwamishinan ’Yan Sandan bisa ziyarar.
Ya yaba da ƙoƙarin Kwamishinan da kuma salon jagorancinsa na taka-tsantsan wajen tabbatar da cewa Jihar Kano ta kasance cikin aminci da tsaro.
Sarkin ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan na dawainiya da babban nauyi, yana mai cewa rundunar ’yan sanda na gudanar da kyakkyawan aiki a jihar.
Ya kuma yi alƙawarin cewa Masarautar Karaye za ta ci gaba da bai wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano cikakken goyon baya da haɗin kai wajen yaƙi da aikata laifuka da sauran matsalolin tsaro.