Shugaban AA Zaura Foundation kuma tsohon ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdussalam Abdulkarim Zaura (AA Zaura), ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a wa’adi na biyu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Hon. Dahiru Ahmad Maiwudaddu, ya fitar, AA Zaura ya ce ci gaba da shugabancin Gwamna Abba zai ba gwamnatin damar kammala shirye-shiryenta da ayyukan raya jihar domin amfanin al’ummar Kano.
Ya bayyana cewa ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar a fannoni daban-daban sun nuna akwai buƙatar a ci gaba da ba ta damar gudanar da manufofinta.
AA Zaura ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da ba gwamnati haɗin kai da goyon baya domin tabbatar da ci gaba, zaman lafiya da bunƙasar jihar.