Jakadan Najeriya a ƙasar Saudiyya, Dakta Yakubu Gambo, ya bayyana cewa akwai wasu ‘yan Najeriya da ke ci gaba da tsare a gidajen yarin ƙasar duk da sun kammala wa’adin hukuncin da kotu ta yanke musu, sakamakon gaza biyan tarar da aka ɗora musu.
Jakadan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Alhamis.
A cewarsa, rashin biyan tarar da kotu ta yanke ne ke hana wasu daga cikin waɗannan ’yan Najeriya samun ’yanci, duk kuwa da cewa sun kammala hukuncin zaman gidan yari.
Bayanin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta NiDCOM, Violet Nwosu, ta sanya wa hannu.
Jakadan ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da abin ya shafa domin nemo hanyoyin magance matsalar tare da ba wa ’yan Najeriya da ke fuskantar irin wannan ƙalubale tallafin da ya dace.