Mahalarta taro na biyu na kasa da kasa kan yaki da kyamar addini Musulunci da Musulmi sun yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe da ƙungiyoyin duniya domin tunkarar barazanar ƙiyayya ga Musulmi da ke ƙara ƙamar.
An gudanar da taron na kwanaki biyu ne a hedkwatar Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da ke Alkahira, Masar.
Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa tare da Ƙungiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Duniya ta Musulunci (ICESCO) ne suka shirya shi.
Taron ya haɗa jami’an gwamnatoci, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, shugabannin addinai, ƙungiyoyin farar hula da wakilan matasa ƙarƙashin taken, “Al’ummomin Musulmi da ke Yammacin duniya da rawar da suke takawa wajen tunkarar kyamar Musulmi.”
Mataimakin Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa mai kula da harkokin sa ido, Ambasada Hussein Hindawi, ya bayyana cewa:
“’Yancin addini da akida haƙƙi ne na asali da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa suka tanada.”
Ya yi gargaɗin cewa kyamar Musulmi ta wuce kasancewa matsalar da ke faruwa lokaci-lokaci, inda ya ce ta koma “babbar matsala ta zamantakewa da siyasa.”
Da yake ambato bayanan Hukumar Tarayyar Turai mai kula da Haƙƙoƙin Dan Adam, Hindawi ya ce kashi 47 cikin 100 na Musulmi a ƙasashe 13 na Tarayyar Turai sun fuskanci wariyar launin fata a shekarar 2024, idan aka kwatanta da kashi 39 cikin 100 a shekarar 2016.
Ya ce kashi 39 cikin 100 sun fuskanci wariya yayin neman aiki, kashi 27 cikin 100 sun sha cin zarafi na wariyar launin fata, yayin da kashi huɗu cikin 100 suka fuskanci hare-haren jiki. Sai dai kashi shida cikin 100 kacal ne suka kai rahoton irin waɗannan hare-hare ga hukumomi.
Hindawi ya ɗora alhakin wannan ƙiyayya kan ra’ayoyin da ke alaƙanta Musulmi da ta’addanci, aikata laifuka da kuma ƙaura ba bisa ƙa’ida ba. Ya buƙaci gwamnatoci, cibiyoyin addini, makarantu, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula su haɗa hannu wajen yaƙi da kalaman ƙiyayya.
A yayin taron kuma, an ƙaddamar da Dandalin Dindindin na Haɗin Gwiwar Ƙasa da Ƙasa don Yaƙi da Nuna Bambanci ga Musulunci da Musulmi, domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe da kuma mayar da shawarwarin da aka gabatar a baya zuwa ayyuka na zahiri.
Haka kuma, mahalarta taron sun tattauna muhimmiyar rawar da ilimi, cibiyoyin addini, ƙungiyoyin farar hula da matasa za su taka wajen bunƙasa haƙuri, mutunta juna da zaman lafiya.