Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dokokin Kano ta amince da kudurin hana makarantu masu zaman kansu...

Majalisar Dokokin Kano ta amince da kudurin hana makarantu masu zaman kansu kara kudi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da Kudirin Gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano na 2026, domin ƙarfafa sa ido da inganta yadda ake gudanar da makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar.

Ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden kudirin shi ne wajabta wa makarantu masu zaman kansu samun amincewar gwamnati kafin su ƙara kuɗin makaranta ko wasu kuɗaɗen hidima.

Majalisar ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe da ake kakaba ba tare da bin ƙa’ida ba.

Haka kuma, kudirin ya tanadi samar da mukamin Babban Sakatare domin ƙarfafa tsarin gudanarwa da inganta ayyukan Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu.

‘Yan majalisar sun ce an yi wannan gyara ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da Kwamitin Ilimi na Majalisar ya gudanar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments