Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa gwamnati na nazarin yiwuwar hana zirga-zirgar babura masu haya (Okada) da kuma Keke Napep a tsakiyar birnin Abuja saboda dalilan tsaro.
A cewar rahoton jaridar Punch, Wike ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙara inganta tsaro da kuma dakile ayyukan masu aikata laifuka a Babban Birnin Tarayya.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya a Abuja.
Sai dai har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe kan aiwatar da wannan shiri ba, domin gwamnati na ci gaba da nazarin yiwuwar ɗaukar matakin.