Kamfanin Dangote Industries Limited ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Sinoma International Engineering Co. Ltd. mai darajar sama da dala miliyan 800, domin faɗaɗa masana’antar simintinsa da ke Itori a Jihar Ogun.
Rahotanni sun ce faɗaɗa aikin zai ƙara ƙarfin samar da siminti a masana’antar, tare da bunƙasa harkokin masana’antu, samar da guraben ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya.
An bayyana cewa wannan sabon zuba jari na daga cikin ƙoƙarin Kamfanin Dangote na faɗaɗa ayyukansa da ƙarfafa matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da siminti a nahiyar Afirka.
Rahoton gidan talabijin na Channels Television ya ce yarjejeniyar na daga cikin manyan ayyukan da ake sa ran za su inganta ƙarfin samar da siminti da biyan buƙatun kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.