Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun kone uba da yaransa a harin da ya hallaka...

Yan bindiga sun kone uba da yaransa a harin da ya hallaka mutum 12 a Sokoto

'Yan bindiga sun shafe sa'o'i 4 su na kai farmaki kauyen jihar Sokoto

Akalla mutum 12 ne suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Lajinge da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun shaida cewa maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar Asabar, inda suka ci gaba da kai hari har zuwa misalin ƙarfe 3:30 na safiyar Lahadi ba tare da jami’an tsaro sun kawo ɗauki ba.

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutum 11 sun mutu sakamakon harbin bindiga, yayin da wata mata mai suna Agada ta rasu bayan ta shiga mummunan firgici a lokacin harin.

Ya ce mutum shida sun mutu bayan maharan sun kewaye ɗakin da suka buya, suka umarce su su fito, amma suka ƙi.

“Sun umarci waɗanda ke cikin ɗakin su fito amma suka ƙi. Sai maharan suka zuba fetur a ɗakin suka kuma buɗe musu wuta. Lokacin da suka yi ƙoƙarin fitowa ta ƙofa, sai suka ci gaba da harbinsu. Daga bisani gawarwakinsu suka ƙone a cikin ɗakin.”

Ya bayyana waɗanda suka mutu a cikin wutar da suka haɗa da mai gidan, Malam Wauro wanda aka fi sani da Malam Roro, da ‘ya’yansa biyu Ukasha da Mujaheed, sai Sufyanu da Sani Shanbami, tare da wani mutum da ya rasa matsuguni wanda ke zaune a gidan.

Majiyar ta ƙara da cewa wani mai suna Lawwali ma an harbe shi a bakin ƙofar gidan yayin da yake ƙoƙarin tserewa, lamarin da ya sa mutum bakwai suka mutu a gidan kaɗai.

Wani ɗan ƙungiyar sintirin al’umma ya ce suna tsaron ƙauyen ne a kusa da makarantar firamare lokacin da suka ji ƙarar harbe-harbe.

“Muna bakin makarantar firamare muna tsaron ƙauyen ne, sai kawai muka ji ƙarar harbe-harbe masu yawa. Kowa ya ruga yana neman mafaka, muna ta sauya wurin ɓuya yayin da harbin ke ƙaratowa.”

Ya ce bayan maharan sun fi ƙarfin masu sintiri, sun shiga gidaje suna kwasar shanu da tumaki.

A cewarsa:

“Sun kafa ɗaya daga cikin bindigoginsu a wani wuri mai muhimmanci yana ci gaba da harbi, yayin da sauran suka shiga gidaje suna satar dabbobi.”

Mazauna sun kuma ce daga baya maharan sun kai hari gidan Malam Wauro, inda suka kashe shi da ‘ya’yansa biyu, suka sace matansa biyu tare da kwashe dukkan shanunsa.

Sun ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka sace ba domin an saki wasu, musamman yara, bayan an tafi da su.

Mazauna ƙauyen sun nuna takaicinsu kan yadda maharan suka kwashe kusan sa’o’i huɗu suna cin karensu ba babbaka ba tare da wani ɗaukin jami’an tsaro ba.

“Sun shafe sa’o’i a ƙauyenmu ba tare da wani ya kawo mana ɗauki ba. Har ma suna tafiya a kan babban titi suna dariya suna shan sigari kamar sun mamaye ƙauyen.”

Sun zargi jami’an tsaro da ke Unguwar Lalle da Dan Tudu, waɗanda ke da tazarar kusan kilomita biyu da Lajinge, da rashin amsa kiran gaggawar da suka yi.

Mazauna sun ce sun sha roƙon gwamnati ta tura jami’an tsaro yankin amma ba a biya musu buƙatarsu ba, tare da bayyana cewa mutum takwas ma an kashe a ƙauyen kimanin makonni uku da suka gabata.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce bai samu labarin harin ba saboda yana tafiya, yana mai cewa zai bincika lamarin da zarar ya isa ofishinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments