Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZaidu Sanusi ya zama ɗan wasan Najeriya na 3 mafi yawan lashe...

Zaidu Sanusi ya zama ɗan wasan Najeriya na 3 mafi yawan lashe kofuna

Zaidu Sanusi ya zama ɗan wasan Najeriya na 3 mafi yawan lashe kofuna

Mai tsaron bayan Super Eagles ta Najeriya, Zaidu Sanusi, ya lashe kofin Portuguese Super Cup karo na huɗu tare da kungiyarsa ta FC Porto, bayan da ƙungiyar ta doke Torreense da ci 1-0 a filin wasa na Estadio EFAPEL Cidade de Coimbra.

Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Denmark, Victor Froholdt, ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Porto nasara a minti na 38, inda ya zura kwallo da kai bayan ya karɓi ƙwallo daga ɗan wasa Pepe.

Sanusi ya buga cikakken mintuna 90 a wasan, yayin da Porto ta lashe kofin Super Cup karo na 25, wanda ya sa ta ƙara zama ƙungiyar da ta fi kowacce lashe manyan kofuna a Portugal, da jimillar kofuna 88, fiye da Benfica.

Tun bayan komawarsa FC Porto a shekarar 2020, Sanusi ya lashe kofuna 10 tare da ƙungiyar, ciki har da gasar lig sau biyu da kuma Super Cup sau huɗu.

Da wannan nasarar, Sanusi ya zama ɗan wasan Najeriya na uku mafi yawan lashe kofuna a matakin ƙungiyoyi, bayan Nwankwo Kanu mai kofuna 14 da John Obi Mikel mai kofuna 12.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments