Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da ƙwace tare da lalata makaman da ake riƙe da su ba bisa ƙa’ida ba domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ribadu ya bayyana haka ne yayin bikin lalata ƙananan makamai da makamai 2,819 da aka ƙwace, ciki har da waɗanda aka daina amfani da su da kuma waɗanda suka lalace.
An gudanar da bikin ne a Barikin Muhammadu Buhari Cantonment da ke Giri, Abuja.
Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin Ɗauka ta Ƙasa ce ta shirya taron, inda ta bayyana cewa tun bayan fara aikinta ta lalata makamai kusan 19,000.
Ribadu, wanda shugaban Shirin Afuwa na Shugaban Ƙasa (PAP), Dr. Dennis Otuaro, ya wakilta, ya ce makaman da ake riƙe da su ba bisa ƙa’ida ba na taimakawa ayyukan ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Ya ce:
“Duk makamin da jami’an tsaro suka ƙwato kuma suka lalata yana nufin an kawar da wata barazana har abada. Muna murƙushe barazana makami bayan makami.”
Ribadu ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wata sabuwar dabarar tsaro da ta mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro, katse hanyoyin samun kuɗin masu laifi da kuma faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.
A cewarsa:
“Wannan tsari ya fara haifar da sakamako a sassan ƙasar nan, daga raunana ƙungiyoyin ‘yan ta’adda zuwa ƙarfafa tsarin tsaron iyakokinmu, kuma ana ci gaba da inganta shi domin fuskantar sabbin barazana.”
Ya ƙara da cewa lalata makaman da aka ƙwace na rage damar da masu aikata laifuka za su samu na amfani da su wajen tada zaune tsaye tare da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro.
NSA ya yabawa Darakta Janar na Cibiyar, DIG Johnson Kokumo mai ritaya da tawagarsa, tare da jinjinawa rundunar ‘yan sanda, sojoji, DSS, Hukumar Kwastam da sauran hukumomin da suka taimaka wajen ƙwato makaman.
Ya ce:
“Irin waɗannan ayyuka da ake gudanarwa suna nuna cewa gwamnati ba ta tsaya kan maganar fatar baki kaɗai ba, tana ɗaukar matakan da ake iya gani domin ƙarfafa amincewar jama’a.”
Ribadu ya buƙaci sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da sauran ‘yan ƙasa su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri cikin lokaci domin dakile barazanar tsaro kafin ta ƙara kamari.