Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar sardaunan Sakoto, Alhaji Abubakar Alhaji

Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar sardaunan Sakoto, Alhaji Abubakar Alhaji

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sardaunan Sokoto, Alhaji Abubakar Alhaji, wanda ya rasu yana da shekaru 85.

A cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen jami’in gwamnati, ƙwararren masani, kuma ɗan kishin ƙasa da ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa tattalin arziki da harkokin diflomasiyyar Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, Masarautar Sokoto, iyalan marigayin, gwamnatin jihar Sokoto da daukacin al’ummar jihar kan wannan babban rashi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments