Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin iya tafiyar da harkokin kuɗin ƙasa, bayan rahotannin da ke nuna cewa gwamnatin ta karɓi bashin da ya zarce iyakar adadin da Majalisar Dokoki ta amince da shi.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce gwamnatin ta ƙara bashin ƙasar zuwa Naira tiriliyan 12.62, wanda ya zarce adadin da aka amince da shi da kusan Naira tiriliyan 4.79.
Atiku ya ce abin mamaki ne yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga daga haraji.
Ya zargi gwamnatin da almubazzaranci, rashin gaskiya da kuma gazawa wajen tafiyar da tattalin arzikin ƙasa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito ta yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan dalilan ci gaba da karɓar basussuka da kuma yadda ake kashe kuɗaɗen da ake samu.
Sai dai gwamnatin tarayya ta sha bayyana a lokuta daban-daban cewa karɓar bashi na daga cikin dabarun samar da kuɗaɗen gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da inganta tattalin arziki.