Sunday, October 18, 2026
HomeTsaro’Yan sandan Sokoto sun dakile harin ’yan bindiga, sun kwato alburusai

’Yan sandan Sokoto sun dakile harin ’yan bindiga, sun kwato alburusai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta sanar da cewa ta dakile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Tauma da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga, tare da kwato wasu alburusai daga hannun maharan.

Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki bayan samun rahoton harin, inda suka yi musayar wuta da maharan.

A cewarsa, matsin lambar da jami’an suka yi ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa zuwa cikin daji, lamarin da ya hana su cimma manufarsu.

Rundunar ta ce an kwato wasu alburusai a wurin bayan da maharan suka tsere, yayin da ake ci gaba da farautar su domin cafke su.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto ya yaba da jajircewar jami’an da suka gudanar da aikin, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma yaƙi da ayyukan ta’addanci a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments