Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya soki Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, kan neman afuwar al’ummar Igbo bisa rawar da mutanen jihar suka taka a lokacin Yaƙin Basasar Najeriya tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970.
Mutfwang ya nemi afuwar ’yan kabilar Igbo ne a wani taro da ya yi da shugabannin al’ummar Igbo daga ƙananan hukumomi 17 na jihar a Jos, inda ya ce an yaudari mutanen Plateau suka shiga yakin. Ya ce ya kamata a rufe shafin baya tare da ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya.
Sai dai Dalung ya ce gwamnan ba shi da ikon ɗaukar matakin neman afuwa a madadin dukkan al’ummar Plateau, yana mai cewa kalaman Mutfwang ba sa wakiltar ra’ayin mutanen jihar baki ɗaya.
A gefe guda, tsohon mai magana da yawun Kudu maso Gabas na Shugaba Bola Tinubu, Josef Onoh, ya goyi bayan matakin Mutfwang, yana mai bayyana neman afuwar a matsayin jarumtar da za ta taimaka wajen sulhu, wanzar da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Onoh ya ce a matsayinsa na zaɓaɓɓen gwamnan Plateau, Mutfwang na da alhakin ɗaukar matakan da za su inganta zaman lafiya tsakanin kabilu, yana mai cewa amincewa da kura-kuran tarihi ba yana nufin raina sadaukarwar wasu ba ne, sai dai hanya ce ta sake gina amana.