Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiRahoton Amurka ya tada kura kan shirin nukiliyar Iran

Rahoton Amurka ya tada kura kan shirin nukiliyar Iran

Rahotannin leken asirin Amurka sun bayyana cewa sabon Jagoran Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, na iya kasancewa mai ra’ayin bunƙasa shirin nukiliyar ƙasar fiye da mahaifinsa, marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

A cewar jami’an Amurka, duk da cewa Mojtaba bai taɓa bayyana a fili cewa yana goyon bayan ƙera makaman nukiliya ba, bayanan leken asiri na nuna yana iya ɗaukar matsaya mai tsauri kan wannan batu.

Rahotannin sun kuma ce Mojtaba ya samu munanan raunuka a lokacin yaƙin baya-bayan nan, amma har yanzu shi ne ke jagorantar gwamnatin Iran, duk da cewa ba shi da irin cikakken iko da tasirin da mahaifinsa ya mallaka.

Haka kuma, an ce Iran ta matsar da wasu na’urorin tace uranium zuwa wurare masu tsaro domin kare su daga yiwuwar hare-hare, yayin da jami’an Amurka suka ce har yanzu ba a samu hujjar cewa Tehran ta sake fara shirin ƙera makaman nukiliya ba.

Sai dai gwamnatin Iran ta ci gaba da musanta duk wani zargi na ƙoƙarin mallakar makaman nukiliya, tana mai cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kawai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments